Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-05-07 11:09:19    
Lardin Sichuan ya gabatar da labarai kan yadda ake sake gina yankunan da aka yi fama da bala'in girgizar kasa

cri

A ran 7 ga wata, gwamnatin lardin Sichuan ta kasar Sin ta kira taron manema labaru domin tunawa da zagayowar ranar cika shekara guda da faruwar girgizar kasa a gundumar Wenchuan a ranar 12 ga watan Mayu na shekarar 2008. Babban sakataren gwamnatin lardin Sichuan, kana kakakin gwamnatin lardin Sichuan Yu Wen da sauransu sun gabatar da labarai na game da sake farfado da yankunan da aka yi fama da bala'in girgizar kasa.

A gun taron, Yu Wei ya bayyana cewa, za a kusan kammala aikin gina gidaje a kauyukan da aka yi fama da bala'in a watan Satumba na shekarar bana, kuma zuwa karshen shekarar bana, za a kammala shi gaba daya. A watan Mayu na shekarar 2010, za a kammala aikin gina gidaje a biranen da aka yi fama da bala'in girgizar kasa a lardin Sichuan.

Yu Wen ya furta cewa, yanzu an riga an soma ayyukan kafa makarantun da bala'in ya lalata kashi 73.3 cikin kashi dari a yankuna 39 da girgizar kasa ta fi yin illa. Zuwa lokacin bazara na shekarar badi, dukkan dalibai za su yi karatu a cikin sabbin gine-ginen makarantu. Dadin dadawa, an tabbatar da cewa za a kammala manyan ayyukan tushe kashi 99 cikin kashi dari a cikin shekaru 2 masu zuwa, kamar ayyukan kiwon lafiya da sauransu. Ya zuwa yanzu, an riga an soma aikin sake ginawa hukumomin kiwon lafiya da na ba da jiyya kashi 46 cikin kashi dari.(Fatima)