Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-05-01 14:55:50    
Ya kasance shekara daya kafin gudanar da bikin baje-koli na Shanghai a shekarar 2010

cri

A ran 1 ga wata, ya kasance saura shekara daya kafin gudanar da bikin baje-koli na Shanghai a shekarar 2010. A gun bikin taya murnar da aka shirya a birnin Beijing, shugaban zaunannen kwamitin majaliar wakilan jama'ar duk kasar Sin Wu Bangguo ya bayyana cewa, gwamnati da jama'ar kasar Sin sun yi alkawari cewa, za su gudanar da bikin baje-koli cikin nasara.

Wu Bangguo ya nuna cewa, kasar Sin za ta kara yin hadin gwiwa tare da kasashen da kungiyoyin daban daban, kuma za su yi kokari wajen sharen fage ga bikin baje-kolin, don tabbatar da za a shirya bikin baje-koli a birnin Shanghai yadda ya kamata. Kasar Sin tana son yin mu'amala tare da kasashen duniya, bikin baje-koli da za a yi a birnin Shanghai zai zaman wani dandali ga jama'ar kasar Sin da jama'ar kasashen duniya wajen neman cimma burin kyautata birnin da zaman rayuwar jama'a da kara dankon zumanci a tsakaninsu.

Babban sakataren birnin Shanghai kuma babban darekatan kwamitin gudanar da bikin baje-koli na kasa da kasa da za a yi a binrin Shanghai Yu Zhengsheng ya yi jawabi cewa, yanzu ana gudanar da aikin sharen fage ga bikin yadda ya kamata, kasar Sin za ta samar da hidima mai kyau ga masu halartar bikin da kafofin watsa labaru da kamfanonin da sauransu.

Ya zuwa ran 1 ga wata, yawan kasashen da suka tabbatar za su halarci bikin baje-koli na kasa da kasa da za a yi a birnin Shanghai a shekarar 2010 ya kai 236. a cikinsu akwai kasashe 20 da ba su kafa dangantakar diplomasiya tare da Sin ba tukuna.(Abubakar)