Wakilinmu ya sami labari daga hukumar kula da harkokin bikin baje koli na duniya na Shanghai cewa, ana yunkurin kammala dukkan ayyukan gine-gine na bikin baje koli na Shanghai ciki har da manyan dakuna hudu a layi daya da wasu gine-gine na wucin gadi da wasu kasashen waje da kungiyoyin duniya suka gina a karshen shekarar 2009.
Bisa shirin da aka tsara, za a gina manyan dakuna guda hudu a layi daya, ciki har da dakin bikin baje koli, da dakin Sin, da cibiyar hukumar kula da harkokin bikin baje koli na duniya, da kuma cibiyar wasanni. A halin yanzu, an kusan kammala wadannan dakuna, kuma ana yi wa cikin dakunan ado, da kwantar da injuna.
An ce, da akwai gine-gine kimanin fiye da dari daya kan bikin baje koli na Shanghai, ciki har da wasu ayyukan din din din kamar manyan dakuna hudu a layi daya, da masaukin bakin masu aikin bikin baje koli, da hanyoyin birnin, da dasa itatuwa da ciyawa a gidan shan iska, kuma da wasu gine-gine na wucin gadi dake kunshe da gine-ginen da kasashen waje da masana'antu suka gina.(Asabe)
|