
A kwanan baya, lokacin da yake ganawa da baki wakilan CRI wadanda suke yin ziyara a lardin Sichuan, Mr. Xian Xiong, mataimakin direktan hukumar zirga-zirga ta lardin Sichuan ya bayyana cewa, hukumomin da abin ya shafa na lardin sun dauki matakai a jere domin kokarin farfado da yawancin tsare-tsaren zirga-zirga da aka lalata su cikin bala'in girgizar kasa da aka yi a shekarar da ta gabata.

An labarta cewa, ya zuwa karshen shekarar da ake ciki, za a kammala ayyukan farfado da zirga-zirga fiye da dari 4 wadanda suka shafi yawan kudaden da aka zuba ya kai fiye da kudin Sin yuan biliyan 56 a lardin Sichuan. Haka kuma ya zuwa yanzu, an riga an kammala ayyukan farfado da tagwayen hanyoyin mota guda 4.
Bisa shirin da aka tsara, yawan ayyukan farfado da tsare-tsaren zirga-zirga a lardin Sichuan ya kai fiye da 470. Kuma yawan kudaden da aka zuba a kan wadannan ayyuka ya kai fiye da kudin yuan biliyan 85. (Sanusi Chen)
|