A ranar 23 ga wata, mataimakin firaministan Sin kuma babban direkta na kwamitin shirya bikin baje-koli na Shanghai Wang Qishan ya bayyana a nan birnin Beijing cewa, dole ne a inganta shawarwari da karfafa hadin gwiwa domin gudanar da aikin share fage kan bikin baje-koli na Shanghai cikin armashi.
Wang Qishan ya fadi haka ne a gun taron kwamitin shirya bikin baje-koli na duniya da za a yi a shekarar 2010 a birnin Shanghai, bikin baje-koli na Shanghai ya kasance wani gagarumin biki ne da za a yi bayan gasar wasannin Olympic ta Beijing a kasar Sin. Dole ne mu samar wa kasashen duniya da kungiyoyin duniya da masana'antu wani dandanli wajen nuna nasarorin da suka samu ta wannan biki.
Za a yi bikin baje-koli na Shanghai daga ranar 1 ga watan Mayu zuwa ranar 31 ga watan Oktumba na shekarar badi, babban taken bikin shi ne "kara jin dadi a birnin Shanghai".(Bako)
|