Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-04-07 21:26:31    
Shugaban kasar Sin ya nuna jaje ga takwaransa na Italiya dangane da girgizar kasa mai tsanani da ta auku a kasar

cri

A ran 7 ga wata, shugaban kasar Sin, Mr.Hu Jintao ya buga waya ga takwaransa na kasar Italiya, Giorgio Napolitano, dangane da girgizar kasa mai tsanani da ta auku a yankin Abruzzo na kasar Italiya, wadda ta yi sanadiyyar mutuwar dimbin jama'a tare da kawo asarorin dukiyoyi.

A madadin gwamnatin kasar Sin da jama'arta da kuma shi kansa ne, Mr.Hu Jintao ya nuna jaje ga Mr. Napolitano da jama'ar da girgizar ta rutsa da su da kuma iyalan wadanda suka riga mu gidan gaskiya sakamakon girgizar. Ya ce, bisa jagorancin shugaba Napolitano da gwamnatin Italiya, tabbas ne jama'ar kasar za su iya farfado da yankunan da bala'in ya shafa.

Har wa yau kuma, a ran 7 ga wata, firaministan kasar Italiya, Silvio Berlusconi ya ce, girgizar kasar da ta auku a yankin Abruzzo a ran 6 ga wata da sassafe ta riga ta yi sanadiyyar mutuwar mutane 207, tare kuma da jikkata wasu sama da 1000.

An ce, yanzu masu aikin agaji kimanin 4000 na gudanar da ayyukan agaji a yankunan da bala'in ya shafa, kuma an kubutad da mutane sama da 100 daga gine-ginen da suka rushe.(Lubabatu)