|
|
|
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye | more>> |
|
|
|
|
|
|
|
(GMT+08:00)
2009-04-03 11:30:56
|
|
(Sabunta)An yi ganawa tsakanin Hu Jintao da shugabannin kasashen Japan da Australia da kuma Brasil har da yarima na Birtaniya
cri
A ran 2 ga wata a birnin London, shugaban kasar Sin Hu Jintao ya gana da firayim ministan kasar Japan Taro Aso, da firayim ministan kasar Australia Kevin Rudd, da shugaban kasar Brasil Luiz Inacio Lula da Silva, da kuma da yarima Charles na kasar Birtaniya.
Yayin da yake ganawa da mista Taro Aso, shugaba Hu Jintao ya bayyana cewa, dangantakar moriyar juna bisa manyan tsare-tsare tsakanin Sin da Japan ta shiga sabon lokacin bunkasuwa. Sin ta ba da shawara da cewa, kamata ya yi kasashen Sin da Japan su ci gaba da yin mu'amala tsakanin shugabannin kasashen biyu, da ci gaba da tabbatar da ra'ayoyin da suka cimma, da kuma yin musayar ra'ayoyi kan dangantakarsu da sauran manyan batutuwa. Ban da wannan, kamata ya yi bangarorin biyu su ci gaba da kara hadin gwiwa kan tattalin arziki da cinikayya da jam'iyyu da hukumomin tsara dokoki da kuma sojoji tsakaninsu. Hakazalika ya kamata kasashen biyu su warware matsalolin da suka faru tsakaninsu don kiyaye dagantakarsu. Kuma Hu Jintao ya bayyana cewa, Sin tana fatan bangarorin biyu za su warware matsaloli ta yin la'akari da sharudan da ke kunshe cikin kudurorin siyasa 4 da kasashen biyu suka daddale.
A gun ganawar, Hu Jintao da Kevin Rudd sun yi musayar ra'ayoyi a kan dangantakar dake tsakanin bangarorin biyu da batutuwa na duniya da na yankuna dake jawo hankalin mutane.
Bugu da kari, lokacin da yake ganawa da Luiz Inacio Lula da Silva, Hu Jintao ya bayyana cewa, kasar Sin tana fatan shugabannin kasashen biyu za su yi mu'amala da kyau, kuma tana fatan yin kokari da Brazil wajen tsara shirin yin aiki tare cikin gaggawa wanda zai jagoranci hadin gwiwa tsakaninsu daga duk fannoni. Ban da wannan kuma, shugaba Hu Jintao ya ce, a gun taron G20, an cimma matsaya kan kara daidaita manufofin tattalin arziki daga duk fannoni na kasa da kasa, da zaunar da gindin kasuwar kudi ta duniya, da kuma yin gyare-gyaren tsarin kudi na duniya. Hakan ya bayyana aniyar shugabannin kasa da kasa ta hadin gwiwa da tinkarar matsala tare. Shugaba Luiz Inacio Lula da Silva ya ce, Sin ta ba da babbar gudummawa ta samun nasarar yin taron G20. A yayin taron, kasashen da suka ci gaba da masu tasowa sun halarci taron cikin adalci, kuma shugabannin kasa da kasa sun amince da sa kaimi kan shawarwarin zagaye na Doha, da yin adawa da matakin kariya da aka dauka wajen yin ciniki.
Har ila yau, shugaba Hu Jintao ya gana da yarima Charles na Birtaniya bisa gayyata, inda bangarorin biyu suka yi musayar ra'ayoyi kan batun kiyaye gine-ginen gargajiya da manya-manyan dazuzzuka gami da sauran batutuwa. (Zainab)
|
|
|