Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-04-03 10:51:46    
Shugaban kasar Sin Hu Jintao ya halarci taron G20 da aka yi a London

cri

A ran 2 ga wata a babban birnin Kasar Birtaniya London, an yi taron koli na kasashe 20 a karo na biyu a kan sha'anin kudi, inda shugaban kasar Sin Hu Jintao ya halarta kuma ya yi mihimmin jawabi.

A gun taron, shugaba Hu Jintao ya yi jawabi mai jigon "Hadin kai don tinkarar matsala tare". Ya bayyana cewa, muhimmin aikin dake gabanninmu shi ne yin iyakacin kokarin farfado da tattalin arzikin duniya, don kaucewa tabarbarewar tattalin arziki; da yin adawa da duk matakin kariya da aka dauka wajen yin ciniki, da kiyaye muhallin yin cinikayya da zuba jari cikin 'yanci; kana da gaggauta ayyukan yin gyare-gyare da sake kafa odar kudi ta duniya. Mista Hu Jintao ya jaddada cewa, kamata ya yi a kara sa ido da hada kan harkokin kudi, da kyautata tsarin hukumar ba da lamuni ta duniya da na bankin duniya, da kuma kara ikon kasashe masu tasowa na ba da shawarwari, kana da kyautata tsarin kudade na duniya.

Bugu da kari, ya ce, don tinkarar matsalar kudi ta duniya, kasar Sin ta dauki manufofin kudi masu yakini wadanda suka dace ta fuskar bullo da shirye-shirye a jere na habaka bukatun jama'a na gida, da sa kaimi kan bunkasuwar tattalin arziki. Ba kawai wadannan shirye-shirye sun kawo tasiri mai kyau ga tattalin arzikin Sin ba, hatta ma sun kawo tasiri mai yakini ga tattalin arziki na shiyyoyi da na duk duniya.

Dadin dadawa, ya nanata cewa, a matsayin wata mamba mai sauke nauyi ta kasashen duniya, kasar Sin tana ta yin kokarin hadin gwiwa da kasa da kasa wajen tinkarar matsalar kudi. Sin za ta ci gaba da daidaita manufofin tattalin arziki na duk fannoni tare da kasashen duniya, da sa kaimi kan yin gyare-gyaren tsarin kudi na duniya don ba da gudummawa wajen farfado da tattalin arzikin duniya.(Asabe)