Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-04-02 11:26:24    
Shugaban kasar Sin Hu Jintao ya gana da shugaban kasar Faransa Nicolas Sarkozy

cri

A ran 1 ga wata, a birnin London, shugaban kasar Sin Hu Jintao ya gana da shugaban kasar Faransa Nicolas Sarkozy.

Hu Jintao ya nuna cewa, in an waiwayi tarihin bunkasuwar dangantaka a tsakanin Sin da Faransa a cikin shekaru 45 da suka wuce, kasashen biyu suna iya yi koyi daga wannan tarihi, mai kunshe su da abubuwa guda 3 masu muhimmanci, wato dole ne a bunkasa dangantakar tsakanin Sin da Faransa daga manyan fannonin a cikin dogon lokaci, kuma dole ne bangarori biyu su bi ka'idar girmama juna da rashin tsoma baki cikin harkokin gida na juna, da kuma yin zama na daidai wa daida da samun moriyar juna, da warware matsalolin gaggawa bisa tushen girmama wa juna, kuma dole ne kara yin mu'amala da yin hadin gwiwa, a kara taka muhimmiyar rawa wajen fuskatar kalubale na duniya, da ba da gudummawa ga tabbatar da zaman lafiya a duniya.

Hu Jintao ya jadadda cewa, a cikin halin sauyawar da kasashen duniya ke yi da matsalar kudi da ke ci gaba da yaduwa, dole ne kasashen Sin da Faransa su ci gaba da bunkasa dangantaka a tsakaninsu, su kuma yi kokari wajen kiyaye ta. Kuma dole ne kasashe biyu su kara yi mu'amala a tsakanin manyan kusoshi na kasashe biyu su kara yin hadin gwiwa a fannonin daban daban, kana su kara yin hadin gwiwa don warware matsalar kudi.

Nicolas Sarkozy ya nuna cewa, ya kan bin manufar Sin daya tak a duniya, kuma a ganinsa, ba za a iya raba Taiwan da Tibet daga kasar Sin ba. Yana yi farin ciki da kasashe biyu suka maido da dagantakar abokantaka na muhimman tsare-tsare, yana fatan za a bunkasa dagantakar yadda ya kamata a fannonin siyasa da tattalin arziki da harkokin diplomasiya da sauransu.

Nicolas Sarkozy ya nuna cewa, kasar Sin tana taka muhimmiyar rawa a tsarin tattalin arziki na duniya, kasar Faransa tana son yin hadin gwiwa tare da kasar Sin don sa kaimi ga yin gyare-gyare cikin hukumomin tattalin arziki na duniya tare.(Abubakar)