Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-04-02 10:06:31    
Shugaban kasar Sin Hu Jintao ya gana da firayim ministan kasar Birtaniya Gordon Brown

cri

A ran 1 ga wata, a birnin London, shugaban kasar Sin Hu Jintao ya gana da firayim ministan kasar Birtaniya Gordon Brown, inda bangarorin biyu suka cimma matsaya kan batun tinkarar matsalar kudi ta duniya, da sa kaimi kan yin gyare-gyaren tsarin kudi na duniya, da kuma bunkasa dangantakar dake tsakaninsu.

Shugaba Hu Jintao ya nuna cewa, a halin yanzu, matsalar kudi ta duniya tana yaduwa, kuma kasuwar kudi tana faduwa, tasirin da matsalar ta kawo wa tattalin arzikin kasa da kasa ya tsananta. Kasashen duniya suna fuskantar wannan matsala ta bai daya wato tinkarar matsalar kudi, da farfado da tattalin arziki. Bangaren Sin ya nuna babban yabo da goyon baya ga bangaren Birtaniya da ya dauki tsauraran matakan tinkarar matsalar. Bangaren Sin zai ci gaba da sauke nauyi tare da bangarori daban daban da za su halarci taron ciki har da Birtaniya don yin kokarin samun ci gaba mai ma'ana a gun wannan taro.

Bugu da kari, shugaba Hu Jintao ya bayyana cewa, wannan matsalar kudi ta kara bayyana kurakurai a cikin tsarin kudi da na tattalin arziki na duniya. Kasa da kasa sun riga sun cimma matsaya kan yin gyare-gyaren tsarin kudi da na tattalin arziki na kasa da kasa, da samar da kyakyawan tsari don bunkasa tattalin arzikin duniya cikin dogon lokaci kuma yadda ya kamata.

Mista Brown ya yi imani da cewa, a karkashin kokarin da kasashen Birtaniya da Sin da sauransu, kasashe ke yi za a samu babban ci gaba mai ma'ana wajen zaunar da gidin kasuwar kudi ta duniya da sa kaimi kan tattalin arzikin kasa da kasa, da yin gyare-gyaren hukumomin kudi na duniya, da kuma taimaka kasashe masu tasowa. Bangaren Birtaniya ya goyi bayan kara kudaden hukumar IMF, da kara musayar kudade, da kuma yin gyare-gyaren tsarin hukumomin kudi na duniya.

Shugaba Hu Jintao ya ce, kasar Sin ta mai da hankali sosai kan bunkasa dangantakar dake tsakanin kasashen biyu, kuma ta mai da dangantakar dake tsakaninsu ta zama daya daga dangantaka mafi muhimmanci dake tsakanin bangarori biyu.
Mista Browan ya bayyana cewa, dangantakar dake tsakaninsu tana bunkasa da kyau. Bangaren Birtaniya ya mai da hankali sosai kan dangantakar abokantaka dake tsakaninsu daga duk fannoni da zumuncin dake tsakaninsu. Birtaniya tana son ci gaba da yin tattaunawa da Sin a kan batun dumamar yanayi da dai sauransu. Ban da wannan kuma, bangarorin biyu sun yi musayar ra'ayoyi kan batutuwan kasa da kasa da na shiyyoyi.(Asabe)