Ran 1 ga wata, shugaba Hu Jintao na kasar Sin ya sauka birnin London, hedkwatar kasar Birtaniya, inda zai halarci taron koli da shugabannin kasashe mambobin kungiyar G20 suka shirya yi kan harkokin kudi a karo na 2 a ran 2 ga wata.
John Prescott, wakilin musamman na firayim ministan Birtaniya kuma tsohon mataimakin firayim ministan Birtaniya shi ne ya karbi shugaba Hu a filin jirgin sama da hannu biyu biyu.
Wannan shi ne karo na 2 da shugaba Hu ya halarci taron koli a tsakanin shugabannin kasashe mambobin kungiyar G20 kan harkokin kudi, bayan da ya halarci wani taron koli na daban da shugabanin suka yi kan kasuwar hada-hadar kudi da tattalin arziki a birnin Washingtong a watan Nuwamba na shekarar bara.
Wang Qishan, mataimakin firayim ministan kasar Sin da sauran jami'an gwamnatin Sin suna cikin tawagar da ta raka shugaba Hu zuwa birnin London.(Tasallah)
|