Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-04-01 08:39:25    
Hu Jintao ya yi hira da manema labaru kan taron G20

cri
A ran 31 ga watan Maris, yayin da yake hira da manema labaru na kamfanin dillancin labaru na Xin Hua a gabannin taron koli na kungiyar kasashe 20 kan sha'anin kudi, shugaban kasar Sin Hu Jintao ya bayyana matsayi da ra'ayinsa kan muhimmanci na wannan taro, da batun tinkarar matsalar kudi, da kuma ci gaba da farfado da tattalin arzikin duniya, kana da halin tattalin arziki da Sin ke ciki.

Shugaba Hu Jintao ya jaddada cewa, taron koli na G20 da za a yi a London yana da muhimmanci sosai wajen kara imanin jama'a da kamfanonin kasar, da zaunar da gindin kasuwar kudi ta duniya, da ci gaba da farfado da tattalin arzikin duniya. A gun wannan taro, bangaren Sin zai sauke nauyi na yin kokarin samun sakamako mai yakini tare da bangarori daban daban da za su halarci taron.

Bugu da kari, shugaba Hu Jintao ya bayyana cewa, a matsayin mamba mai daukar nauyi ta kasashen duniya, kasar Sin ta yi ta yin iyakacin kokarin hadin kai da kasa da kasa wajen tinkarar matsalar kudi. Sin za ta ci gaba da karfafa daidaita manufofin tattalin arziki daga duk fannoni da kasa da kasa, da sa kaimi kan yin kwaskwarima kan tsarin kudi na duniya, da yin yunkurin kiyaye tsarin yin cinikayya a tsakanin bangarori daban daban, don ba da gudummowa kan farfado da tattalin arzikin kasa da kasa.

Dadin dadawa, ya ce, duk da fuskantar matsalar kudi, muna yin imani da cewa muna da sharuda masu kyau da karfin ci gaba da bunkasa tattalin arzikin Sin yadda ya kamata. Kuma Sin za ta ci gaba da bin manufar bude kofa ga kasashen ketare, da tafiyar da manyan tsare-tsaren bude kofa wadanda za su kawo moriyar juna.(Asabe)