Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-03-30 16:36:02    
Ra'ayin da aka bayar na wai mutanen Tibet sun zama tsirarru ba shi da tushe

cri
A cikin wani rahoton da cibiyar nazarin ilmin Tibet ta kasar Sin ta bayar dangane da ci gaban tattalin arziki da zamantakewa a ran 30 ga wata, an ce, wasu mutane da kungiyoyin duniya da ba na gwamnati ba sun yi kururuwa cewa sabo da mutanen Han masu yawa sun shiga jihar Tibet, mutanen Tibet sun zama tsirarru wannan zance ne ba shi da tushe.

A cikin rahoton, an ce, tun da jihar Tibet ta samun 'yanci kai zuwa shekarar 2008, yawan mutanen jihar Tibet ya karu daga miliyan 1.2 ko fiye a shekarar 1959 zuwa miliyan 2.8 ko fiye a shekarar 2008, kuma yawan mutanen kabilar Tibet ya karu daga miliyan 1 zuwa miliyan 2.7 a shekarar 2008. Ban da haka kuma, ba a aikata manufar kayyade yawan haihuwa a jihar Tibet ba. Kuma bayan da aka gudanar da manufar bude kofa ga kasashen ketare da yin gyare-gyare, mutanen sauran yankunan kasar Sin sun je jihar Tibet don yin kasuwanci, amma yawan mutanen kabilar Tibet ya karu fiye da kashi 90 na duk mutane a jihar Tibet. Ban da haka kuma, dalilin da ya sa yawan mutanen jihar Tibet ya karu cikin sauri shi ne karuwar haihuwar mutanen kabilar Tibet da sauri.(Abubakar)