Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-03-30 16:20:49    
(Sabunta)Masu halartar taron tattaunawar addinin Buddha na duniya a karo na biyu sun isa Taipei

cri
A ran 30 ga wata, an ci gaba da yin taron tattaunawar addinin Buddha na duniya a karo na biyu a Taipei. Yanzu tawagar masu halartar taron ta farko ta riga ta isa Taipei.

An ba da labari cewa, wakilai kimanin dubu daya sun tashi daga birnin Nanjing domin zuwa Taipei kai tsaye cikin jiragen sama hudu a yau. Ana sa ran cewa, jirgin sama na karshe zai isa filin jiragen saman Taoyuan na Taipei da karfe hudu na yamma a yau.

A ran 30 ga wata da dare, hukumomin da abin da ya shafa za su yi liyafa a gidan abinci mai suna Yuanshan na Taipei don maraba da masu halartar taron tattaunawar addinin Buddha. Za a yi tattaunawa a kananan dakula guda takwas game da harkokin addinin Buddha kamarsu kyautata ruhun mutane na kiyaye muhalli daga zuciya da nuna ban kulawa na ba da taimakon addinin Buddha a ran 31 ga wata a jami'ar Huafan ta Taipei da Tudun Fagu da sauran wurare.

Yanzu, hukumomi da abin da ya shafa na yankin Taiwan sun riga sun share fagen karbar masu halartar haron. An ce, hukumomin da suka karbi bakuncin wannan taro sun yi kira ga masu aikin sa kai 1500 da su shiga aikin karbar bakunci na wannan taro, kuma sun bayar da horaswa ga masu aikin sa kai a kwanakin baya. Ban da wannan kuma, hukumomin sun shirya da kyau a fannonin samar da abinci da dakunan kwana da dai sauransu.(Asabe)