Jaridar People's Daily ta Sin ta ba da labari cewa, za a yi taron koli na kudi na kasashe 20 a karo na biyu daga ran 1 zuwa ran 2 ga watan Afrilu a birnin London na Birtaniya. Yayin da yake hira da manema labaru game da wannan a kwanan baya, ministan kudi na Sin Xie Xuren ya bayyana cewa, ba kawai Sin ta dauki matakai a jere cikin gaggawa na sa kaimi kan ci gaba da tattalin arzikinta ba, hatta ma ta shiga shirin tallafin tattalin arziki na duniya tare da kasashen duniya, alal misali, ta goyi bayan hukumar ba da lamuni ta duniya da bankin raya Asiya da sauransu su kara zuba jari don ba da taimako ga sabbin kasuwanni da kasashe masu tasowa da su kara karfin tinkarar matsalar kudi, da sa kaimi kan hadin gwiwa na kudi tsakanin kasashen yankin gabashin Asiya.
Bugu da kari, mista Xie Xuren ta ce, matsalar kudi da kasa da kasa ke fuskanta ta kara bayyana wasu kurakuran tsarin kudi na duniya da ake yin amfani da shi yanzu. Ya kamata kasashen duniya su yi yunkurin sa kaimi kan yin kwaskwarima ga hukumomin kudi na duniya kamar su IMF da bankin duniya, da gaggauta tsara lokaci da taswirar yin kwaskwarima, don kara daga matsayin kasashe masu tasowa da wakilinsu da ikonsu na ba da shawarwari.
Dadin dadawa, Xie Xuren ya ce, kamata ya yi a gaggauta tsara tsarin kudaden kasa da kasa, da kara yin amfani da kadade na iri-iri don zaunar da gindin tsarin kudaden kasa da kasa.(Asabe)
|