Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-03-28 18:16:35    
Shugabannin Sin sun halarci bikin baje kolin kayan tarihi na cika shekaru 50 da yin gyare-gyaren dimokuradiyya a Tibet

cri

A dab da ranar tunawa da 'yantar da miliyoyin bayi manoma a Tibet, kwanan nan, bi da bi ne shugabannin kasar Sin, ciki har da Hu Jintao da Wu Bangguo da Wen Jiabao da Jia Qinglin da Li Changchun da Xi Jinping da Li Keqiang da He Guoqiang da kuma Zhou Yongkang sun je cibiyar baje kolin al'adun kabilun kasar Sin da ke nan birnin Beijing, don kallon nune-nunen kayayyakin tarihi na cika shekaru 50 da yin gyare-gyaren dimokuradiyya a Tibet da ake gudanarwa a nan wurin.

A gun bikin baje kolin, Hu Jintao, shugaban kasar Sin, ya yi nuni da cewa, gyare-gyaren dimokuradiyya da aka yi a Tibet yau da shekaru 50 da suka wuce, sauyin tsarin zaman al'umma ne mafi muhimmanci da kuma ma'ana a tarihin Tibet, haka kuma wani babban taimako ne da jama'ar kasar Sin suka bayar ta fannin bunkasa hakkin bil Adam a duniya. Manyan sauye-sauyen da suka faru a Tibet bayan gyare-gyaren sun shaida mana cewa, Tibet ba ta iya samun babban cigaban tattalin arziki da zaman al'umma ba, haka kuma al'ummarta ba su iya zama masu gida na kasar Sin da kuma jin dadin zaman alheri ba, sai dai su kasance karkashin jagorancin jam'iyyar kwaminis ta Sin da kuma cikin kasa mai gurguzu.

Hu Jintao ya kuma jaddada cewa, kamata ya yi a ci gaba da bin hanyar gurguzu da ke da sigar musamman ta Sin da kuma hanyar neman cigaba da ke da halin musamman na Sin da Tibet, sa'an nan, a gaggauta cigaban tattalin arzikin Tibet da kyautata zaman rayuwar al'ummar Tibet, musamman ma manoma da makiyaya a Tibet, da kuma kara inganta kwanciyar hankali a Tibet, don samar wa Tibet makoma mai kyau.(Lubabatu)