A gabannin ranar tunawa da 'yantar da miliyoyin bayi manoma ta farko, mazauna kauyen Kesong na garin Changzhu na yankin Shannan, wanda ya kasance kauye na farko da aka kaddamar da gyare-gyare ta hanyar dimokuradiyya a jihar Tibet, sun fitar da wata wasika ga miliyoyin 'yantattun bayi manoma a jihar, inda suka yi kira ga jama'a da su kawar da cikas, da more zaman jin dadinsu.
A shekara ta 1959, bayi manoma sama da dari 4 a kauyen Kesong sun kafa kungiyar hadin-gwiwar manoma ta farko a jiahr Tibet, daga baya, a karkashin jagorancin jam'iyyar kwaminisanci ta kasar Sin ne aka soma yin gyare-gyare ta hanyar dimokuradiyya a jihar. Sabo da haka, ana kiran kauyen Kesong "kauye na farko da aka yi gyare-gyare ta hanyar dimokuradiyya a jihar Tibet".
Mai bada tayin bayyana wasikar, kana tsohon bawa manomi Sonam Dondrup ya ce, shawararsa ta nuna wasika ga miliyoyin 'yantattun bayi manoma ta sami amincewa daga daukacin mazauna kauye. Makasudin bayyana wannan wasika shi ne, a bayyana hakikanin halin da ake ciki a jihar Tibet.(Murtala)
|