Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-03-27 21:29:05    
Jaridar People's Daily da Kamfanin dillancin labaru na Xinhua sun yi sharhin murnar ranar tunawa da 'yantar da miliyoyin bayi manoma

cri
A ran 28 ga wata, jaridar People's Daily ta kasar Sin ta buga sharhin murnar ranar tunawa da 'yantar da miliyoyin bayi manoma. Sharhin ya ce, a ran 19 ga watan Janairu na wannan shekara, taron majalisar wakilan jama'ar jihar Tibet ya zartas da kudurin tsai da ranar 28 ga watan Maris na kowace shekara da ta zama ranar tunawa da 'yantar da miliyoyin bayi manoma a Tibet, wannan ya bayyana burin al'ummar Tibet da kuma al'ummar kasar Sin baki daya.

Sharhin ya ce, gyare-gyaren dimokuradiyya da aka gudanar a Tibet wani muhimmin sauyin tsarin al'umma ne a tarihin Tibet, kuma a sakamakon gyare-gyaren, miliyoyin bayi manoma da sauran bayi sun sami 'yanci, har ma sun zama masu gida a sabuwar Tibet. Gyare-gyaren sun kuma kasance wani babban taimakon da Sin ta bayar ga harkar hakkin dan Adam ta duniya, kuma ma'anarsu da muhimmancinsu ya kai ga duk wani aiki na yin watsi da tsarin mallakar bayi da aka yi a duniya.

Har wa yau kuma, kamfanin dillancin labaru na Xinhua shi ma ya bayar da sharhi, inda ya isar da fatan alheri ga jama'ar da ke zaune a Tibet su miliyan 2 da dubu 870. Sharhin ya ce, a cikin shekaru 50 da suka gabata, ci gaban Tibet ta fannonin tattalin arziki da zaman al'umma ya jawo hankalin duniya. An tabbatar da ikon jama'ar Tibet na tafiyar da harkokinsu su da kansu, sa'an nan, tattalin arzikin yankin ma ya bunkasa kwarai da gaske. Ban da wannan, an kyautata zaman rayuwar jama'a tare da kuma da ba da kariya ga al'adun gargajiyar al'ummar wurin. Jama'ar Tibet na samun cikakkiyar girmamawa ta fannin bin addininsu.

Sharhin ya kara da cewa, babu wanda zai iya hana burin jama'ar Tibet na bin zaman rayuwa mai kyau da kuma amincinsu na bin hanyar gurguzu da ke da sigar musamman ta Sin a karkashin jagorancin jam'iyyar kwaminis ta Sin.(Lubabatu)