Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-03-27 21:00:21    
Ziyarar kungiyar wakilan jihar Tibet a kasashen Amurka da Canada ta sami sakamako mai kyau

cri
Bayan da kungiyar wakilan jihar Tibet ta kammala ziyarar aikinta a kasashen Canada da Amurka, a ranar 27 ga wata, ta shirya wani taron manema labaru a nan birnin Beijing, kuma shugaban kungiyar, rayayye buddah Shingtsa Tenzinchodrak ya bayyana cewa, wannan ziyara ta sami sakamako mai kyau.

Shingtsa tenzinchodrak ya bayyana cewa, hukumomi daban daban na Amurka da Canada ba su nuna shakku ko kadan ba ga tarihin jihar Tibet na kasancewar wani yanki na kasar Sin da ba za a iya raba shi da kasar Sin ba. Amma a sa'i daya kuma, kungiyar wakilan ta lura da cewa, sabo da farfaganda da labarin karya da Dalai ya baza a duniya bisa matsayinsa na jagoran addini hade da rashin sani a kan tarihin jihar Tibet daga jama'a, a kan tambaye su ko ana kiyaye hakkin dan Adam a jihar Tibet. A yayin ziyarar, kungiyar wakilan ta yi bayani filla-filla a kan ainihin halin da jihar Tibet ke ciki.

Haka kuma Shintsa Tenzinchodrak ya bayyana cewa, a cikin shekarun 50 da suka wuce, bayi manoma da yawansu ya kai kashi 95 cikin kashi 100 na al'ummar Tibet ba su da 'yancin kansu da sauran hakkoki. Amma bayan yin gyare-gyaren demokuradiyya a shekarar 1959, jama'a na samun moriyar hakkin bil 'Adam, da hakkin yin zabe. Bayan shekarar 1959, jihar Tibet ta sami yanayi mai kyau a cikin tarihi, jama'a na jin dadin hakkokinsu.

Kana kuma Shingtsa Tenzinchodrak ya bayyana cewa, yayin da kungiyar wakilan take ganawa da wasu mutane, sun bayyana cewa, ranar tunawa da 'yancin bayi manoma na da ma'ana daya tare da ranar tunawa da 'yancin bayi bakaken fata na Abraham Lincoln.(Bako)