Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-03-27 20:29:33    
An yi taron tattaunawa don tunawa da cika shekaru 50 da 'yantar da miliyoyin bayi manoma a Tibet a nan birnin Beijing

cri

A ranar 27 ga wata a nan birnin Beijing, an shirya taron tattaunawa don tunawa da cika shekaru 50 da 'yantar da miliyoyin bayi manoma a Tibet. Zaunannen mamban ofishin siyasa na kwamitin tsakiya na Jam'iyyar Kwaminis ta Sin, kuma shugaban majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Mr. Jia Qinglin ya halarci taron, kuma ya yi jawabi.

Mr. Jia Qinglin ya nuna cewa, soke tsarin bauta na gargajiya na mulki irin na gwamutsa siyasa da addini a Tibet, ya kasance gyare-gayren zaman al'umma mafi ma'ana da aka yi a tarihin jihar Tibet, ya sanya jihar Tibet shiga wani sabon babi. Shi ne kuma wani muhimmin taimakon da jama'ar kasar Sin ta bayar kan sha'anin hakkin Bil Adam na duniya, ya bude hanyar samun bunkasuwar siyasa ta dimokuradiyya a Tibet. A waje daya kuma, wannan muhimmiyar alama ce ta ayyukan soke tsarin bayi manoma na duniya, hakan ya sa kaimi ga ci gaban wayewar kai na dan Adam.

Bayan haka kuma, Mr. Jia Qinglin ya jaddada cewa, yanzu bunkasuwar tattalin arziki da al'umma ta jihar Tibet tana kan matsayin sabon masomi a tarihinta, ya kamata a yi kokari kan ciyar da samun babbar bunkasuwar tattalin arziki gaba, da ba da tabbaci da kyautata zaman rayuwar jama'ar jihar. A waje daya kuma, ya kamata a tsaya tsayin daka kan kiyaye zaman karko na zaman al'ummar Tibet, da kuma tabbatar da manufofin kabilu, da addinai na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin. Kazalika kuma, Mr. Jia Qinglin ya nanata cewa, dukkan ayyukan zuga da kungiyar Dalai Lama take yi, ba za su canja hakikanin yanayin Tibet, wanda wani yankin kasar Sin ne ba za a iya raba shi da kasar ba, kuma ba za su iya kawar da manyan nasarorin da aka samu ta fuskar yunkurin gyare-gyaren dimokuraddiya a cikin shekaru 50 da suka wuce ba. (Bilkisu)