A kwanan baya, ana dab da karatowa ranar 28 ga wata, wadda rana ce ta tuna baya ga manoma bayi na jihar Tibet da suka samu 'yanci kai, shugaban tawagar wakilan Sin dake Kungiyar Tarayar Turai kuma jakada Song Zhe ya aika wasika zuwa wakilan majalisar dokoki na nahiyar Turai, inda ya bayyana sakamakon da jihar Tibet ta samu a cikin shekaru 50 da suka wuce bayan yin gyare-gyaren dimokuradiyya da manufofi game da Dalai Lama da gwamnatin kasar Sin ta dauka, don fadakar da su bisa hakikanin hali kuma daga dukkan fannoni dangane da jihar Tibet.
A cikin wasikar da Song Zhe ya aika, ya yi amfani da hakikanin abubuwa da yawa don shaida aikin gyare-gyaren dimokuradiyya a jihar Tibet da aka yi a shekaru 50 da suka wuce da cewa, shi ne muhimmin aiki na tarihin kiyaye bunkasuwar jihar Tibet, kuma shi ne abu mafi muhimmanci na tarihin hakkin Dan Adam na duniya.
A sa'i daya kuma, Song Zhe ya nuna cewa, Dalai Lama a matsayin babban wakilin sarkin bayi na tsohuwar jihar Tibet, bai daina yin aikin yanke jihar Tibet daga kasarSin ba.
Song Zhe ya nanata cewa, Tibet wata jiha ce ta kasar Sin, kuma ba za a iya ware jihar Tibet daga kasar Sin ba, kuma batun Tibet ya shafi harkokin cikin gida na Sin. Kasar Sin tana nuna kiyayya yin na'am din kasashe ko kungiyoyi da su yin amfani da batun Tibet don sa hannu a kan harkokin gida na kasar. A cikin wasikar, ya bayyana fatan wakilan majalisar dokokin na nahiyar Turai da su nuna girmamawa ga kasar Sin bisa ikonta na mulkin kai da cikakken ikon mallakar yankin kasa, da kuma nuna girmamawa ga damuwar jama'ar kasar Sin, su kuma fahimci hakikanin halin da jihar Tibet take ciki, sannan su yi yin kokari tare kasar Sin, don kiyaye da sa kaimi ga bunkasuwar dangantakar tsakanin Sin da nahiyar Turai yadda ya kamata.(Abubakar)
|