Darektan sassan ilmin zamantakewar al'umma na jami'ar Los Angeles ta yamma ta Amurka ya taba zuwa jihar Tibet a shekarar 2004. A ran 27 ga wata, za a gabatar da bayanin da ya rubuta mai suna "Kyautatuwar zaman rayuwa" a jaridar People's Daily.
A lokacin, Farfesa ya je jihar Tibet tare da mutane 10 daga hukumar sada zumunta ta Guangzhou a birnin Los Angeles na Amurka. Sun isa birnin Lhasa da na Shannan da sauransu, kuma sun kai ziyara a Fadar Potala da Gidan ibada mai suna Jokhang, inda suka kalli shirye-shiryen kabilar Tibet da dandana Hamburger na naman Yak.
A cikin bayanin, Farfesa ya bayyana cewa, jihar Tibet tana da kyaun gani sosai, jama'a suna zaman lafiya, ko kadan ba kamar yadda wasu kafofin watsa labaru na yammacin kasashe suka fadakar ba. Wasu 'yan kabilar Tibet sun gaya wa Farfesa cewa, gwamnatin Sin tana ba da taimako wajen samun ruwan sha mai inganci da kafa gidaje da sauransu. Suna nuna gamsuwa ga kyautatuwar zaman rayuwa. Kuma ana girmamawa 'yancin bin addininsu yadda ya kamata.(Fatima)
|