Ran 28 ga wata rana ce ta farko ta tuna baya ga manoma bayi na jihar Tibet da suka samu 'yanci kai. A ran 26 ga wata, jaridar People's Daily ta kasar Sin ta bayar da bayanin edita mai suna "abu mafi muhimmanci na tarihin hakkin Dan Adam na duniya", inda aka nuna cewa, aikin yin gyare-gyaren dimokuradiyya a jihar Tibet da aka fara yi a shekarar 1959, wani muhimmin abu ne na tarihin aikace-aikacen kawar da tsarin manoma bayi na duniya. kuma aikin yin gyare-gyaren dimokuradiyya a jihar Tibet ya samu amincewa daga kasashe daban daban.
A ran 10 ga watan Maris a shekarar 1959, kungiyar da ke karkashin jagorancin Dalai Lama ta yi juyin mulkin soja don kiyaye tsarin manoma bayi. Tun daga ran 28 ga watan Maris, gwamnatin kasa ta jagoranci jama'ar Tibet don yaki da dakarun da suka yi juyin mulkin soja da aiwatar gyare-gyaren dimokuradiyya a jihar Tibet, kuma gwamnatin ta cire tsarin manoma bayi, sakamakon haka, manoma bayi da yawansu ya wuce miliyan 1 sun samu 'yanci kai. A sa'i daya kuma, tun da gwamnatin ta cire tsarin hada siyasa da addinai, jama'ar jihar Tibet suka samo 'yancin bin addinin, kuma aka kafa mulkin ikon jama'a na dimokuradiyya, don kiyaye ikon jama'ar jihar Tibet.
A cikin bayanin edita, an ce, aikin yin gyare-gyaren dimokuradiyya a jihar Tibet ya haifar da sakamakon bunkasuwar hakkin Dan Adam na kasar Sin, kuma ya samu amincewa daga kasashe daban daban.(Abubakar)
|