Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-03-26 13:55:32    
Jakadu na kasa da kasa dake Sin sun halarci bikin baje koli na cika shekaru 50 da yin gyare-gyaren dimokuradiyya a Tibet

cri
Bisa gayyatar ma'aikatar harkokin waje ta Sin, jakadu fiye da 60 na kasashen waje da na hukumomin duniya dake Sin sun halarci bikin baje koli na cika shekaru 50 da yin gyare-gyaren dimokuradiyya a Tibet a ran 25 ga wata a birnin Beijing.

Jakadan Ghana dake Sin Akwasi Agyeman Agyare ya ce, a gun bikin, ya gano hakikanin halin da aka samu na babban ci gaba a Tibet. Dalilin da ya sa rukunin Dalai Lama ya kan ta da rudani a kan batun Tibet shi ne yana damuwa da ganin yadda aka bayyana karyar da ya yi a fili.

Jakadan Somaliya dake Sin Mohamed Ahmed Awil ya bayyana cewa, wadannan hotuna shaidu ne dake bayyana dukkan abubuwan da suka abku a cikin shekaru 50 da suka gabata.

Ban da wannan kuma, jakadan Cuba dake a kasar Sin Carlos Miguel Pereira ya ce, gwamnatin Sin ta ba da babbar gudummawa wajen bunkasa Tibet. Hakan ya bayyana nufin gwamnatin Sin na bunkasa Tibet da cika alkawarinta ga Tibet.(Asabe)