A ran 24 ga wata a birnin Washington, tawagar wakilan masanan Sin kan harkokin Tibet wadda a halin yanzu ke ziyara a kasar Amurka, ta yi shawarwari kan batun Tibet tare da daliban kasar Sin da ke dalibta a Amurka da Sinawa mazauna kasar, inda suka bayyana tarihin Tibet da cigabanta da kuma namijin kokarin da gwamnatin kasar Sin ta yi wajen kiyaye al'adun Tibet da kuma yanayin halittun wurin, sun kuma musanta sukan da wasu kasashen yammaci suka yi wa kasar Sin ba gaira ba dalili ta fannin kare muhallin Tibet.
Shugaban tawagar kuma shugaban hukumar nazarin ilmin kabilu da na dan Adam da ke cibiyar nazarin zaman al'umma ta kasar Sin, Mr.Hao Shiyuan ya ce, a cikin wani dogon lokaci, gwamnatin kasar Sin da kananan hukumomin kasar sun yi namijin kokari wajen daukaka cigaban tattalin arziki da al'adu da zaman al'umma a Tibet, kuma Tibet ta sami kashi 93% zuwa 94% na kasafin kudinta daga tallafin gwamnatin kasar Sin da kuma kananan hukumomin wurare daban daban na kasar.
Hao Shiyuan ya kara da cewa, a wajen tsara cigaban Tibet, har kullum gwamnatin kasar Sin na mayar da kare al'adun yankin Tibet da yanayin halittunta a wani matsayi mai muhimmanci. Yanayin halittu ya sami kariya sosai a Tibet, har ma ingancinsa ya zo na farko a kasar Sin. Amma duk da haka, wasu kasashen yammaci sun yi fatali da gaskiyar abin, har ma sun yi suka ga manufar Sin ta kare muhallin Tibet, abin ko kadan ba shi da dalili.(Lubabatu)
|