Wani bayanin da kamfanin dillancin labaru na Xinhua ya bayar a ran 24 ga wata ya yi nuni da cewa, miyagun ayyukan da rukunin masu neman jawo baraka na Dalai Lama yake yi na neman manoma su kauracewa aikin noman rani ba zai yi tasiri ba illa kara bayyana mugun nufinsa na jawo baraka.
Bayanin ya ci gaba da cewa, zaman jama'a ya dogara kan abinci, kuma sanin kowa ne abinci na da muhimmancin gaske. Duk da haka, an yi watsi da aikin noman rani a wasu yankunan noma da makiyaya na lardin Sichuan sabo da ruda hankali manoma da rukunin Dalai Lama ya yi. Yanzu an shiga lokacin noma rani a kasar Sin, idan ba a yi noman rani cikin lokaci ba, to ba za a girbi kome ba, har ma manoma da makiyaya za su shiga wahala. A hakika, zuga manoma da makiyaya su kauracewa aikin noman rani wata dabara ce ta rashin hadin kai da rukunin Dalai Lama ya kan yi amfani da ita wajen ruda hankulan jama'a da yi wa ci gaban tattalin arziki da zamantakewa na kasar Sin zagon kasa. Wannan matakin da rukunin Dalai Lama ya dauka wani mugun aiki ne na rashin kula da moriyar dimbin manoma da makiyaya, ya kuma kara tsiraita makarkashiyar rukunin Dalai Lama ta neman jawowa kasar Sin baraka ta hanyar amfani da jama'a.
Bayanin ya bayyana cewa, kwamitin jam'iyya da gwamnati na wuri sun dauki matakai da dama cikin lokaci na tono makarkashiyar masu aikata laifuffuka da kiyaye odar zama, da yi wa manoma jagora wajen noman rani, da samar da takin zamanin da manoma suke bukata a kyauta bayan an samu alamun daina aikin noman rani. Aikin noman rani ya kankama daga gabas zuwa yamma, daga arewa zuwa kudu a wadannan yankuna bayan da manoma da makiyaya suka gano muhimmancin aikin noman rani.(Asabe)
|