A ranar 23 ga wata, a nan birnin Beijing, shugaban kasar Sin Mr. Hu Jintao ya bayyana cewa, bangaren kasar Sin ya dora muhimmanci sosai a kan taron koli a karo na 2 na shugabannin rukunin kasashe 20 masu karfin tattalin arziki da za a yi a birnin London, haka kuma yana fata zai yi kokari tare da bangarorin da abin ya shafa don ingiza sakamakon da za a samu a gun taron.
A wannan rana, bayan da Mr. Hu ya yi shawarwari tare da takwaransa na kasar Uruguay Tabare Ramon Vazquez Rosas. Bangarorin biyu sun daddale wata sabuwar yarjejeniyar hadin gwiwa tsakaninsu, inda kasar Uruguay ta amince da cikakken matsayin tattalin arziki na kasar Sin.
Mr. Hu ya ce, Sin tana fatan inganta hadin gwiwa tare da kasashe masu tasowa ciki har da kasar Uruguay, don magance kalubalen da rikicin hada-hadar kudi ta duniya ya kawo, da kiyaye da sa kaimi ga zaman lafiya da kwanciyar hankali da samun bunkasuwa a dukkan duniya.
Haka kuma, Mr. Hu Jintao ya yaba wa danganatakar da ke tsakanin Sin da Uruguay da manufar kasar Sin daya tak a dukkan duniya da Uruguay ke tsayawa da tsayayyen goyon baya da take nuna wa kasar Sin a kan batutuwan Taiwan da Tibet da dai manyan batutuwan duniya. Vazquez ya bayyana cewa, kasar Uruguay za ta ci gaba da tsayawa tsayin daka kan manufar kasar Sin daya tak a dukkan duniya, yana fatan kara inganta hadin gwiwa da mu'amala tsakanin kasashen biyu a kan dangantakar kasashen biyu da dangantakar kasashen duniya daga dukkan fannoni.(Bako)
|