Wata majiya daga shafin Internet na bukin baje-koli na kasa da kasa ta ce, kasar Belize wadda ke arewa maso gabashin tsakiyar nahiyar Amurka, ta tabbatar da cewa, za ta halarci bukin baje-koli na kasa da kasa da za'a shirya a birnin Shanghai na kasar Sin a shekara ta 2010. Zuwa ranar 23 ga wata, akwai kasashe da kungiyoyin kasa da kasa da adadinsu ya kai 233 wadanda suka bada tabbacin halartar bukin baje-koli na kasa da kasa da za'a yi a birnin Shanghai.
Kasar Belize, da sauran kasashen yankin Caribbean guda 10, gami da kungiyar hadin-kan kasashen Caribbean za su shirya nune-nune cikin hadin-gwiwa a dakin nune-nune na kungiyar hadin-kan kasashen Caribbean.
Har yanzu kasar Sin ba ta kulla dangantakar diflomasiyya a tsakaninta da kasar Belize. A halin da ake ciki yanzu, yawan kasashen da ba su kulla huldar diflomasiyya tare da kasar Sin ba wadanda suka tabbatar da halartar bukin baje-kolin ya kai 17.(Murtala)
|