 Tun daga zamanin da aka fara bikin nune-nunen cika shekaru 50 da yin gyare-gyaren dimokuradiyya a jihar Tibet ta kasar Sin a ran 24 ga watan Fabrairu, yawan mutanen kasar Sin da suka halarci bikin ya wuce dubu 100.
A gun wannan biki, an nuna hotuna fiye da 500 da kayayyaki fiye da 180, kuma an nuna mawuyacin halin da jama'ar Tibet suka kasance a ciki kafin yin gyare-gyaren dimokuradiyya, kuma an sake nuna duhun da ake ciki na aiwatar da tsarin manoma bayi da tsarin gargajiya a tsohuwar jihar Tibet da yanayi na bayan yin gyare-gyaren dimokuradiyya, jama'ar Tibet sun samu yanci kuma sun zama masu gidajen kansu a jihar Tibet.
Bisa labarin da aka bayar, an ce, an yi hasashen cewa, yawan mutanen da za su halarci bikin nune-nunen cika shekaru 50 da yin gyare-gyaren dimokuradiyya a jihar Tibet da za a shafe kwanaki 50 ana yi ya haura dubu 200.(Abubakar)
|