Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-03-18 16:14:45    
'Yantar da bayi miliyan daya nasara ce da ake cimmawa a fannin kiyaye hakkin dan adam a jihar Tibet

cri
A ran 18 ga wata a birnin Beijing, masanin ilmin Tibet na Sin Tenzin Chepa ya bayyana cewa, 'yantar da bayi miliyan daya babbar nasara ce da aka samu a fannin kiyaye hakkin Bil'adam a jihar Tibet.

Shekarar bana shekara ce ta cikon shekaru 50 da aka yi gyare-gyaren dimokuradiyya a jihar Tibet. Ran nan an gudanar da taron karawa juna sani na tunawa da "Cikon shekaru 50 da yin kwaskwarima irin ta dimokuradiyya a jihar Tibet" a birnin Beijing. A gun taron, Tenzin Chepa ya furta cewa, bayan da aka 'yantar da bayin, an samu babbar kyautatuwa a zaman alummar jihar Tibet. A cikin shekaru 50 da suka gabata, an sami babbar nasara a fannin tarbiyya a jihar. Kuma an inganta zaman rayuwar al'adu na jama'ar Tibet sosai. An kiyaye kayayyakin fasahohin gargajiya da adabi na jihar Tibet masu dimbin yawa.

Tenzin Chepa ya bayyana cewa, mayar da ran 28 ga watan Maris na kowace shekara a matsayin ranar tunawa da 'yantar da bayi miliyan daya a jihar Tibet, muhimmin abu ne a cikin tarihin bunkasuwar jihar Tibet, kuma alama ce ta samun babbar nasara wajen kiyaye hakkin Bil'adam a jihar.(Fatima)