A ran 15 ga wata, manemi labaru ya kai ziyara a mazaunin Tongjian da na Ejietang dake titin Gama Gongsang a birnin Lhasa, inda ake ganin cewa, 'yan kabulu daban daban suna zama tare cikin lumana.
Madam Wangyin Zilan, 'yar kabilar Tu, ta kasance mazauniyar Tongjian, asalinta jihar Qinghai. A shekarar 1995 ta je birnin Lhasa tana sana'ar tela da gyaran takalma ga mazauna wurin, Wangyin Zilan ta bayyana cewa, yanzu tana samun kudin Sin yuan 50 zuwa 60 a kowace rana, ba ma kawai wannan ya iya biyan bukatun zaman rayuwarta ba, hatta ma ta samu rarar kudi. Kuma a ranar farko ta kalandar kabilar Tibet a kasar Sin, tana samun aiki sosai, sabo da abokan kabilar Tibet da yawa suna zuwa domin dinka sabbin tufafi.
A mazaunin Ejietang, 'yan jarida sun gamu da Yang Hongying, 'yar kabilar Han ta kasar Sin, wadda take yin ciniki har shekaru 10 a birnin Lhasa. A shekarar 2000, ta je birnin Lhasa ta tafiyar da wani kantin wanke tufafi, kuma ta fi samun kudi bisa lokacin da take yin aikin gona a garinta.
Darektar ofishin kula da harkokin mazauna titin Gama Gongsang madam Drolma Yangscan ta furta cewa, 'yan kabilu daban daban na Sin suna zama tare cikin lumana. Ta ce, a shekarar bana, sun gudanar da ayyuka da yawa, misali, a lokacin shagalin bazara, 'yan kabilar Tibet sun je gidajen 'yan kabilar Han domin nuna fatan alheri, a ranar farko ta kalandar kabilar Tibet, 'yan kabilar Han suna nuna fatan alhari ga 'yan Tibet a gidajensu. Dadin dadawa kuma, suna gudanar da ayyukan sada zumunta da yawa. (Fatima)
|