Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-03-15 17:18:39    
'Yantar da bayin manoma ya dace da ainihin makasudin addinin Buddha, in ji Panchen na 11

cri
Ran 15 ga wata, a fadar al'adun al'umma ta Beijing, Panchen Lama na 11 Erdeni Qoigyi Gyibo ya halarci taron nune-nune kan 'cika shekaru 50 da aka yi gyare-gyare ta fuskar dimokuradiyya a jihar Tibet mai cin gashin kanta', inda ya ce, 'yantar da bayin manoma ya dace da ainihin makasudin addinin Buddha.

Panchen Lama na 11 ya bayyana cewa, nune-nunen ya sake shaidawa munin tsarin bautawa na gargajiya da aka bi a Tibet a da da kuma zaman rayuwar mazauna Tibet a wancan lokaci. Ya kuma nuna manyan sauye-sauyen da aka samu a jihar Tibet a cikin shekaru 50 da suka wuce, inda miliyoyin bayin manoma suka samu 'yancin kai, sun iya raya kansu, sun iya tafiyar da harkokin Tibet da kansu. Abubuwan gaskiya sun fi abubuwan da aka fada. Ba za a iya bai wa bayin manoma mutunci da 'yancin kai a matsayin wani mutum ba, sai dai jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin ita kawai.

Sa'an nan kuma, a lokacin da wakilinmu yake ziyara a gidan ibada na Jokhang da na Sera, ana gudanar da harkokin addini yadda ya kamata, kuma dimbin 'yan Buddha sun bayyana masa burinsu na kin yarda da samun tashe-tashen hankali.

Losang Chosphel, nagartaccen dan Buddha a gidan ibada na Sera ya yi nuni da cewa, yanzu gwamnatin tsakiya ta kasar Sin ta yi kirar raya zaman al'ummar kasa mai jituwa. Wannan ya cimma matsayi da samun jituwa da addinin Buddha ya kira a samu. Wasu 'yan tawaye, ciki har da wasu 'yan Buddha sun yi tashe-tashen hankali a ran 14 ga watan Maris na shekarar bara, sun raunana jituwar da ake neman samu. Bai kamata su yi haka ba .(Tasallah)