Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-03-13 21:45:50    
Sashen kula da harkokin waje na majalisar NPC ya nuna fushi da kin yarda kan kudurin da majalisar Turai ta zartas game da Tibet

cri
A ran 13 ga wata, wani jami'in sashen kula da harkokin waje na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin, ya yi jawabi, inda ya nuna fushi da kin yarda kan zartas da kudurin da ya shafi batun Tibet da majalisar Turai ta yi.

Jami'in ya ce, a ran 12 ga wata, duk da rashin amincewar bangaren Sin, majalisar Turai ta kare aniyar zartas da kudurin da ya shafi batun Tibet, kan yunkurin mayar da batun a matsayin batu na kasa da kasa. Da kakkausar murya ce 'yan kasar suka nuna fushinsu da kin yarda kan irin aiki na tsoma baki cikin harkokin gidan Sin, wanda ya lalata huldar da ke tsakanin Sin da Turai da kuma bakanta ran jama'ar Sin.

Jami'in ya kara da cewa, sabanin da ke tsakanin Sin da Dalai Lama ba batu ne na tsakanin kalilu ba, haka kuma ba na addini ba ne, balle ma na kiyaye hakkin dan Adam, amma wani muhimmin batun da ke shafar mulkin kan kasar Sin da cikakkun yankunan kasar. Majalisar wakilan jama'ar Sin na sanya muhimmanci sosai a kan huldar da ke tsakaninta da majalisar Turai, kuma tana neman majalisar da ta yi watsi da matsayin da ta dauka na ba daidai ba, kuma ta tsaya ga nuna adalci, kuma ta kara gudanar da ayyukan da za su amfana wa huldar da ke tsakanin Sin da Turai.(Lubabatu)