Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-03-12 20:48:45    
Idan al'ummar Tibet sun ji dadin zaman rayuwarsu, dukkan makarkashiyar da 'yan -a-ware suka kulla aikin banza ne

cri
A ranar 12 ga wata, shugaban jihar Tibet mai cin gashin kanta kuma wakilin majalisar wakilan jama'a ta kasar Sin Qiangba Puncog ya bayyana a nan birnin Beijing cewa, aikin da ke gaban kome ne wajen yaki da 'yan a ware da masu neman 'yancin kai na Tibet shi ne, a gaggauta bunkasa jihar Tibet da kara kokarta wajen kyautata zaman rayuwar al'ummar Tibet, hakan jama'a za su iya jin dadin zaman rayuwarsu. Muddin dai mu kara karfafa hadin gwiwa tsakanin al'ummar Tibet, kome danyen aiki da 'yan-a-ware suka yi aikin banza ne.

Qiangba Puncog ya bayyana cewa, ko a da, ko kuma yanzu, ko nan gaba, rukunin Dalai mai kokarin kawo wa Sin baraka da abokan gaba na yada jita-jita kuma sun kawo wa lahani ga gwamnatin tsakiya ta Sin da jihar Tibet. Game da wadannan danyen aiki, abin da ya fi muhimmanci ga kasar Sin shi ne a yi kokari domin gudanar da ayyukanta.

Qiangba puncog ya bayyana cewa, abin da ya fi muhimmanci wajen cimma nasarar bunkasa tattalin arziki na jihar Tibet shi ne a kara kyautata zaman rayuwar manoma na jihar Tibet da kara kudin shigar manoma, ta hakan za a iya bunkasa zamantakewar al'ummar Tibet tare da sauran unguwanni, ta hakan za a iya ba da tabbaci ga hadin gwiwa tsakanin al'umomin Tibet da bunkasuwa da kafa wani yanayi na daidaici da taimakawar juna da jituwa, da aza wani harsashi wajen kawo zaman lafiya da jituwa a jihar Tibet.(Bako)