Kwanan baya, majalisar wakilan Amurka ta zartas da wani shirin kudurin da ya shafi Tibet, kuma kakakin ma'aikatar harkokin waje ta Sin, Mr.Ma Zhaoxu ya bayyana a ranar 12 ga wata a nan birnin Beijing cewa, Sin ta riga ta bayyana rashin jin dadinta ga Amurka, ta kuma nemi majalisar dokokin Amurka da ta gyara kuskurenta nan da nan, kuma ta daina yin amfani da batun Tibet wajen tsoma baki cikin harkokin gida na Sin, kada ta yi abin da zai lalata huldar da ke tsakanin Sin da Amurka.
An ce, kwanan baya, majalisar wakilan Amurka ta zartas da wannan kuduri, inda ba gaira ba dalili ta yi suka kan manufar gwamnatin Sin game da Tibet, har ma ta yi kirari ga Dalai Lama wanda ya dade yana ayyukan jawo baraka ga kasar Sin.
A yayin da yake amsa tambayoyin wakilinmu a gun taron manema labarai, Mr.Ma Zhaoxu ya jaddada cewa, kudurin ya yi biris da ainihin gaskiya, kuma ya saba wa ka'idoji na huldar da ke tsakanin kasa da kasa, ya kuma tsoma baki cikin harkokin gida na kasar Sin. Gwamnatin kasar Sin da jama'arta na nuna kyama sosai kan hakan.(Lubabatu)
|