A ran 11 ga wata, a birnin Beijing, bayan da wakilin majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta jama'ar Sin kuma shugaban addinin Buddah na gidan ibada mai suna Qambalin da ke a jihar Tibet Tsonlo Champa Kedup ya halarci bikin nuna ci gaban da aka samu a Tibet a cikin shekaru 50 da suka wuce bayan da aka yi mata gyara fuska, ya bayyana wa manema labaru cewa, jama'ar jihar Tibet suna da 'yancin bin addinai da ba a taba gani ba.
Tsonlo Champa Kedup ya nuna cewa, Tibet wani bangare ne na kasar Sin wanda ba za a iya raba shi da kasar Sin ba, yanzu jama'ar Tibet suna jin dadin rayuwarsu, wannan hakikanin abu ne.
Bayan tashin hankalin da ya auku a ran 14 ga watan Maris na shekarar bara, Tsonlo Champa Kedup ya bayyana wa masu bin addinin Buddah cewa, ayyukan da rukunin Dalai ya yi, sun karya tsarin Buddah, kuma sun bata sunan addinin Buddah.(Abubakar)
|