Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-03-11 20:22:21    
Sin na nuna adawa da katsalandan da Amurka ta yi a harkokin cikin gidanta dake shafar jihar Tibet

cri

Ranar 11 ga wata a nan birnin Beijing, mai magana da yawun ma'aikatar harkokin waje ta kasar Sin Mista Ma Zhaoxu ya bayyana cewa, harkokin Tibet, harkokin cikin gida ne na kasar Sin, nuna yatsa ga kasar Sin kan batutuwan dake shafar jihar Tibet, da tsoma baki cikin harkokin cikin gida na kasar da Amurka ta yi, ya bakanta ran jama'ar kasar Sin. Sin ta riga ta nuna adawa da rashin jin dadi ga kasar Amurka a kan wannan lamari.

A ranar 10 ga watan da muke ciki, kakakin fadar White House da na ma'aikatar harkokin waje ta kasar Amurka sun gabatar da jawabi da bayar da sanarwa a kan batutuwan dake shafar jihar Tibe ta kasar Sin, inda suka zargi manufofin da gwamnatin kasar Sin ke aiwatarwa kan jihar, da bukatar kasar Sin da ta yi shawarwari tare da Dalai Lama. Yayin da yake amsa tambayoyin 'yan jarida, Mista Ma Zhaoxu ya ce, Sin ta bukaci gwamnatin Amurka da ta mutunta ka'idojin kasa da kasa, da daina duk wani yunkuri na yin shisshigi cikin harkokin gida na kasar Sin ta hanyar yin amfani da batutuwan dake shafar Tibet, don kaucema lalata huldodin kasashen biyu.(Murtala)