Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-03-11 16:42:54    
Jihar Tibet mai ikon tafiyar da harkokin kanta ta bayar da ka'idar kiyaye fadar Potala

cri
Bayan yin nazarin tsawon watanni 8, a ran 10 ga wata gwamnatin jihar Tibet mai ikon tafiyar da harkokin kanta ta bayar da ka'idar kiyaye fadar Potala. Wannan ka'idar ta kasance daya tak da Jihar Tibet mai ikon tafiyar da harkokin kanta ta bayar don kiyaye gine-ginen tarihi.

A cikin ka'idar an tsara shirin musamman na ko-ta-kwana don kiyaye fadar Patala da kayyade adadin mutanen da za su shiga fadar Potala, kuma an tsara mamufofin yanke hukunci ga aikace-aikacen saba wa dokar. Wani jami'in jihar Tibet mai ikon tafiyar da harkokin kanta ya nuna cewa, idan ba su yi amfani da tsauraran hanyoyi don tafiyarwa da kiyaye fadar Potala ba, ba za a nuna kima ga kayayyakin tarihi ba, kuma 'yan baya ba za su fahimci tarihi da al'adu na fadar Potala ba.

Tun daga watan Yuli na shekarar 2006, sabo da sana'ar yawon shakatawa ta jihar Tibet ta samu bunkasuwar sosai bayan an gama aikin shimfida hanyar jirgin kasa da ta hada lardin Qinghai da jihar Tibet, gwamnatin jihar Tibet ta kayyade cewa, yawan mutane da za su shiga fadar Potala ba zai wuce 2300 ba a ko wace rana.(Abubakar)