An sami labaru daga hukumar kula da yawon shakatawa ta Tibet cewa, yawan mutanen dake yawon shakatawa a Tibet da yawan kudin da aka samu a farkon watannin biyu na shekarar da muke ciki ya karu bisa makamancin lokaci na shekarar da ta gabata. Sana'ar yawon shakatawa ta Tibet tana kawar da mummunan tasirin da arangama da ta barke a ran 14 ga watan Maris a shekarar bara ta kawo, kuma sana'ar ta fara bunkasuwa daga duk fannoni.
Daga watan Janairu na bana zuwa watan Fabrairu, yawan mutanen gida da na waje dake yawon shakatawa a Tibet ya kai dubu 120, ya karu da 4.8%, yawan kudin shiga da aka samu ya kai kudin Sin Yuan miliyan 99, ya karu da 0.6% bisa makamancin lokaci na bara.
Sakamakon rikicin da aka yi a ran 14 na watan Maris na bara, yawan mutanen gida da na waje dake yawon shakatawa a Tibet ya kai miliyan 2 da dubu 240 a shekarar da ta gabata, ya ragu da 40% bisa makamancin lokaci na shekarar 2007. Yawan kudin shiga a fannin yawon shakatawa ya kai kudin Sin Yuan biliyan 2 da miliyan 200 wanda ya ragu da kashi 50 cikin dari bisa makamancin lokaci na shekarar 2007.(Asabe)
|