Yayin da yake halartar shawarwarin tawagar wakilan Tibet a gun taron shekara shekara na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin, shugaban kasar Sin, Mr.Hu Jintao ya jaddada cewa, kamata ya yi Tibet ta aiwatar da jerin manufofin da gwamnatin kasar Sin ta tsara game da harkokin Tibet, kuma ta dora muhimmanci a kan samun ci gaba da kwanciyar hankali, don tabbatar da bunkasar tattalin arziki da zaman al'umma, da kuma tsaron kasa da kwanciyar hankalin zaman al'ummar Tibet, haka kuma don kyautata zaman rayuwar al'ummomi daban daban.
Mr.Hu Jintao ya jaddada cewa, kamata ya yi Tibet ta bi hanyar ci gaba da ke da sigar musamman na Sin da na Tibet, sa'an nan, ya kamata ta kyautata zaman rayuwar jama'a, ta yadda jama'a 'yan kabilu daban daban za su iya jin dadin nasarorin da aka samu daga yin gyare-gyare a gida da bude kofa ga kasashen waje. Bayan haka, ya kamata ta inganta tushen kiyaye dinkuwar kasa, don tabbatar da kwanciyar hankali mai dorewa a yankin.(Lubabatu)
|