Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-03-09 10:57:25    
Ana sa ran cewa, mutane miliyan 70 za su halarci taron baje-kolin kasa da kasa na birnin Shanghai a shekarar 2010

cri

A ran 8 ga wata, mataimakin shugaban kwamitin gudanarwa na taron baje-kolin kasa da kasa na birnin Shanghai na shekarar 2010 Zhou Hanmin ya bayyana a birnin Beijing cewa, ana sa ran mutane miliyan 70 ne za su halarci taron.

A gun taron maneman labaru na shekara-shekara na majalisar ba da shawarwari kan harkokin siyasa ta kasar Sin a wannan rana, yayin da yake amsa tambayoyi daga 'yan jarida na kasar Japan game da ko yawan masu halartar taron baje-kolin kasa da kasa na Shanghai ya wuce na birnin Osaka wato miliyan 64, Zhou Hanmin ya bayyana cewa, mu mai da taron baje-kolin kasa da kasa na Osaka a matsayin misalin koyo, domin yawan masu halartar taron ya fi na kowane taron baje-kolin kasa da kasa, kuma taron ya sa kaimi da kafa yankin tattalin arziki na Osaka a kasar Japan. Ya ce, bisa kiddidigar da aka samu kan yawan masu halartar taron Shaghai, ana sa ran cewa, mutane miliyan 70 ne za su halarci taron baje-kolin kasa da kasa na birnin Shanghai, wadanda a cikinsu kashi 5% zuwa 10% mutanen kasashen waje ne.(Zainab)