Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-03-08 19:28:08    
Yawan kasashe da kungiyoyin da za su halarci babban bikin baje koli na duniya ya kai sabon matsayi a tarihi

cri

Ran 8 ga wata, Mr. Zhou Hanmin mataimakin direkatan kwamitin shirya babban bikin baje koli na duniya na Shanghai ya nuna cewa, ya zuwa wannan rana, akwai kasashe 185 da kungiyoyin kasa da kasa 46 sun riga sun tabbatar da za su halarci babban bikin baje koli na duniya, wannan ya kai sabon matsayi a tarihi.

A gun taron manema labaru na majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin da aka yi a nan birnin Beijing, Mr. Zhou Hanmin ya ce, an kiyasta cewa yawan mutanen da za su ziyarce babban bikin zai kai miliyan 70, kuma kashi 5 zuwa kashi 10 daga cikinsu su ne 'yan bude ido na kasashen waje.

A gun taron manema labaru, Mr. Wan Jifei direkatan gudanarwa na babban bikin ya nuna cewa, matsalar hada-hadar kudi ta duniya ba ta yi mummunan tasiri sosai ba ga babban bikin na Shanghai. Ya zuwa yanzu, dukkan kasashe da kungiyoyin ba wanda ya janye shirinsa na harlarci babban bikin. Ko da yake wasu kasashe sun sami matsala saboda karancin kudi, kasar Sin mai masaukin baki za ta ba da taimako da goyon bayan da abin ya shafa. [Musa Guo]