Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-03-07 16:52:21    
Jama'ar Tibet suna da cikakken ikon mulkin yankunansu da kansu da ikon bin addini

cri
A kwanan baya, lokacin da yake ganawa da wakiliyarmu, Mr. Pasang Dondrup, mataimakin shugaban majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta jihar Tibet ta kasar Sin ya bayyana cewa, yanzu jama'ar Tibet suna da cikakken ikon mulkin yankunansu da kansu da kuma ikon bin addini cikin 'yanci. Mr. Pasang Dondrup ya ce, "Yanzu, rukunin Dalai ya yi jitajita a duniya, cewar wai babu hakkin dan Adam a jihar Tibet yanzu. Wannan ba abin gaskiya ba ne. Alal misali, yanzu yawancin wakilan majalisar wakilan jama'a ta jihar Tibet jami'ai da jama'a ne na kabilun Tibet. Sannan yawan jami'an kabilun Tibet ya kai kusan kashi 70 cikin kashi dari daga cikin dukkan jami'an da suke aiki a jihar Tibet. Muna da cikakken ikon mulkin yankunanmu da kanmu."

Lokacin da yake zantawa kan batu ko jama'ar Tibet suke bin addini cikin 'yanci? Mr. Pasang Dondrup ya bayyana cewa, "Idan kana bin addinin halal, ko shakka babu, gwamnatin tsakiya ta kasar Sin tana kiyaye su. Kuma manufofin da muke bi suna kuma amince da jama'a da su bi addini na halal cikin 'yanci." (Sanusi Chen)