Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-03-06 17:00:33    
Jihar Tibet za ta kara zuba jari don kyautata zaman rayuwar jama'a

cri
Shekarar bana, jihar Tibet mai cin gashin kanta za ta kara zuba jarin da yawansa ya kai kudin Sin Yuan biliyan 1.5 a sha'anin kiyaye zaman rayuwar jama'a, domin kara ba da tabbaci ga kyautata zamantakewar alumma, kuma idan aka kwatanta wadannan kudaden da za ta bayar da na shekarar bara, ya ninka sau daya ke nan.

Bisa kididdigar da ofishin kula da harkokin kudi na jihar Tibet ya samu, an ce, a shekarar bana, jihar Tibet za ta yi amfani da rabin kudaden da za ta bayar a sha'anin kiyaye zaman rayuwar jama'a, watau Yuan miliyan 720 wajen samar da inshora ta aikin jinya ga ma'aikata da mutane a birane da garuruwa, da ba da kudin ragwame ga inshora na tsoffin mutane, da ba da inshora wajen haihuwa da dai sauran fannonin da suka shafi tsarin zamantakewar al'umma. Haka kuma za a yi amfani da kudaden da yawansu ya kai kudin Sin Yuan miliyan 157 don kara samar da guraben aikin yi da horaswa, da samun guraben aikin yi, kuma wannan adadi ya ninka sau 1.5 bisa na makamancin lokaci na bara. Game da wani muhimmin aiki wajen kiyaye zaman rayuwar jama'a, watau hayar gidaje masu rahusa, jihar Tibet za ta samar da kudaden rangwame da yawansu ya kai Yuan miliyan 100.

Haka kuma, jihar Tibet za ta ci gaba da kara samar da kudade ga mutane masu albashi kalilan, kuma za ta kara zuba jari don sa ido kan magunguna da abinci da dai sauran kayayyaki.(Bako)