Domin tunawa da cika shekaru 50 da aka yi gyare-gyare na demukuradiyya a jihar Tibet ta kasar Sin, a ranar 5 ga wata, tasha ta 4 ta gidan telebijin din kasar Sin watau CCTV-4 ta nuna fim din "Labarun bayi manoma a jihar Tibet" a nan birnin Beijing.
A cikin wannan fim, an yi amfani da muhimman labarun tarihi da aka sani game da aikin yin gyare-gyare na demokuradiyya a jihar Tibet, domin bayyana tsarin mulkin danniya kuma na rashin imani na hade mulkin siyasa da addini tare a jihar Tibet, kana kuma ya bayyana mana manyan nasarorin da bayi manoma a jihar Tibet suka samu, bayan da aka aiwatar da tsarin yin gyare-gyare na demukuradiyya a cikin shekaru 50 da suka gabata a jihar Tibet.
Bisa labarin da muka samu, an ce, an fassara wannan fim ne zuwa harsunan Turanci da Faransanci da Spananci, kuma nan ba da dadewa ba, za a nuna su a tashoshin telebijin na Turanci da Faransanci da Spananci a gidan telebijin din kasar Sin. (Bako)
|