Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-03-06 14:25:01    
Sin ta dauki matakai na farfado da masana'antun kasar

cri

A ran 5 ga wata, ministan masana'antu da sadarwa na kasar Sin Li Yizhong ya bayyana a birnin Beijing cewa, ana yin bincike kan yadda za a gudanar da shirin kyautata da bunkasa masana'antu, musamman a fannin farfado da masana'antun.

Li Yizhong ya ce, wa'adin shirin kyautata da bunkasa masana'antu za a shaye shekaru 3 ne kawai, musamman a shekarar bana. Yanzu ana yin bincike kan yadda za a gudanar da shirin. A ganinsa, a karkashin kokarin duk kasar Sin, wasu masana'antu na gwamnatin kasar da na yankuna sun riga sun samu kyautatuwa. Amma rikicin hada-hadar kudi na duniya bai zo karshe ba tukuna, sabo da haka, halin da ke ciki a kasar mawuyaci ne.

A kwanakin baya, an tattauna da zartas da shirin kyautata da bunkasa manyan masana'antu 10 a taron zaunannen membobin majalisar gudanarwa ta kasar Sin. Kuma shirin ya yi babbar ma'ana ga kiyaye bunkasuwar tattalin arziki yadda ya kamata da habaka bukatu cikin gida da kuma kara samun bunkasuwa a nan gaba.(Zainab)