Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-03-05 16:20:55    
Kasar Sin za ta ci gaba da zurfafa hadin gwiwa da kasashen ketare don tinkarar matsalar kudi tare

cri
A ran 5 ga wata a nan Beijing, firayim ministan kasar Sin Wen Jiabao ya bayyana cewa, kasar Sin za ta ci gaba da zurfafa hadin gwiwa da kasashen ketare don tinkarar yaduwar matsalar kudi, da ciyar da gyare-gyaren tsarin kudi na duniya gaba, da yin adawa da ra'ayin kariyar cinikayya da zuba jari, don gaggauta farfado da tattalin arzikin kasa da kasa.

Mista Wen Jiabao ya ce, a sabuwar shekara, kasar Sin za ta ci gaba da aiwatar da manufofinta na shimfida zaman lafiya da raya kasa da hada kai da kasashen ketare, da rika bunkasa kasa ta hanyar zaman lafiya, da kuma tsayawa kan manufar diplomasiyya ta zaman lafiya mai cikakken mulkin kai, kana da ci gaba da aiwatar da manufar bude kofa mai kawo moriyar juna. Ban da wannan kuma, za ta kara mu'amala ta zumunci da kasashen ketare don kafa yanayi mai kyau ga samun bunkasuwar tattalin arzikin kasar.

Sin za ta yi la'akari da babbar moriyar jama'ar kasar da ta saura kasashen duniya don ci gaba da taka muhimmiyar rawa wajen shawo kan muhimman batutuwan dake janyo hankalin duk duniya. Dadin dadawa, gwamnatin Sin da jama'arta suna fatan yin kokari tare da kasa da kasa don tinkarar matsalar kudi da dai sauransu.(Asabe)