Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-03-05 12:15:49    
Sabonta: An bude taron shekara-shekara na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin

cri

An bude taron shekara-shekara na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin a nan birnin Beijing, hedikwatar kasar Sin, a ranar 5 ga watan Maris. Wen Jiabao, firayin ministan kasar, ya halarci taron majalisar wadda ke da ikon koli a kasar Sin, inda ya ba da rahoto kan aikin gwamnatin kasar, ya ce, gwamnatin za ta fi mai da hankali kan aikin tinkarar rikicin hada-hadar kudi, da raya tattalin arzikin kasar cikin sauri da kuma nuna daidaito, a shekarar da ake ciki. Rahoton da ya bayar ya nuna imanin da gwamnatin kasar Sin ke da shi na shawo kan rikicin hada-hadar kudi.

Cikin rahotonsa, Mista Wen ya ce, gwamnatin kasar Sin ta shimfida matakai da yawa don samun damar cimma burinta na raya tattalin arzikin kasar cikin sauri da zaman karko. Za ta kara zuba jari, da rage yawan tara haraji, da raya sana'o'I daban daban, da ingiza kirkiro sabuwar fasaha, da kyautata aikin ba da tabbaci ga zaman rayuwar jama'a, da kuma kara guraben aiki a birane da kauyuka, da dai makamantansu, ta yadda za a habaka bukatun da ke da su a gida, da kara karfin tattalin arzikin kasar, da kuma ciyar da zaman rayuwar jama'ar kasar gaba. (Bello Wang)