Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-03-05 11:56:42    
Gwamnatin kasar Sin za ta samu gibin kudi na Yuan biliyan 950 a shekarar bana

cri
A ranar 5 ga watan Maris, Wen Jiabao, firayin ministan kasar Sin ya sanar da cewa, yawan gibin kudi da gwamnatin kasar Sin za ta samu a shekarar bana zai kai Yuan biliyan 950, wato kimanin dalar Amurka biliyan 138.9, sai dai jimillar ba ta fi kashi 3% na yawan kudin kayayyakin da aka samar a kasar Sin a shekara daya ba.

Yayin da Mista Wen ke yin bayani kan dalilin da ya sa aka kara samun gibin kudin, ya ce, baitulmalin kasar ya shiga cikin wani mawuyacin hali, wato a bangare daya, ba a samu saurin karuwar tattalin arziki iri na da ba sa kamakon rikicin hada-hadar kudi, sa' an nan manufar rage yawan tara haraji ita ma ta zama nauyin da ke kan gwamnatin.A dayan bangare kuma, don inganta tattalin arziki,da raya zaman rayuwar jama'a, gwamnatin Sin za ta kara zuba kudi a fannoni da yawa. Kuma don daidaita matsalar karancin kudi, gwamnatin kasar Sin ta shirya tinkarar samun gibin kudi, inda ta sa Yuan biliyan 750 a baitulmalin kasar, da kuma ba da takardun lamuni na Yuan biliyan 200 don tallafa wa gwamnatocin shiyya-shiyya.

Game da wannan gibin kudin, Mista Wen ya ce, ba zai yi illa ga tattalin arzikin kasar Sin ba, domin kasar tana da karfi na daukar wannan nauyi.(Bello Wang)