Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-03-05 11:19:57    
Kudin da gwamnatin kasar Sin ta zuba ga bunkasa yankunan karkara ya karu da 40%

cri
A shekarar 2008, gwamnatin kasar Sin ta ware Yuan biliyan 595.5 don raya aikin gona, da yankunan karkara, da kuma amfana wa manoma. Idan an kwatanta yawan kudin da wanda aka zuba a shekarar 2007, za a ga ya karu da biliyan 163.7, wato kashi 37.9% ke nan.

Wen Jiabao, firayin ministan kasar Sin, ya gabatar da jimillar ne yayin da yake ba da rahoto kan aikin gwamnatin kasar a bikin bude taron shekara-shekara na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin, a ranar 5 ga watan Maris da safe, inda Mista Wen ya ce, gwamnatin kasar Sin ta tsaya kan karfafa aikin raya aikin gona da yankunan karkara, da amfana wa manoma, cikin shekarar da ta wuce. Tallafin kudin da gwamnatin kasar Sin ta zuba don yankunan  karkara kadai ya kai Yuan biliyan 103, wanda ya ninka na shekarar 2007 sau daya, in ji mista Wen.

Wen Jiabao ya kara da cewa, kasar Sin ta kara farashin amfanin gona da gwamnatin ke amfani da shi yayin da take sayen kayayyakin daga hannun manoma da kashi 20% a shekarar 2008, sa'an nan ta karfafa aikin raya gonaki, da aikin ban ruwa, don raya aikin gonan kasar a dukkan fannoni. (Bello Wang)